Zabura 48:1 - Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji mai girma ne, Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu, A kan tsattsarkan dutsensa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”