12 Za ka taimake ni domin ina yin abin da yake daidai, Za ka sa ni a gabanka har abada.
12 Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada.
Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya, Yakan kafa su har abada tare da sarakuna, A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.
Gama Ubangiji zai raba mugaye da ƙarfinsu, Amma zai kiyaye mutanen kirki.
Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.
Raina yana manne maka, Ikonka yana riƙe da ni.
Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,
Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni, Gama na dogara gare ka.
Na ce, “Ina kan fāɗuwa,” Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
Zan gan ka domin ni adali ne, Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.
Za ka nuna mini hanyar rai, Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki, Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.
Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna, Ka kuwa warƙar da ni.