11 Zan sani kana jin daɗina, Domin ba za su rinjaye ni ba,
11 Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
Ya ƙwace makaman masarauta da na masu iko, ya kunyata su a fili, da ya yi nasara a kansu a kan gicciyen.
Sai mu gode wa Ubangiji, Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.
Ku raira waƙa ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Gama ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannun mugaye.
Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa, Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.
Ka nuna mini alherinka, ya Ubangiji, Sa'an nan su waɗanda suke ƙina za su sha kunya, Sa'ad da suka ga ka ta'azantar da ni, Ka kuma taimake ni.
A gare ka nake dogara, ya Allah. Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa, Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!
Kada ka bar su su ce wa kansu, “Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!” Kada ka bar su su ce, “Mun rinjaye shi!”
Ba ka bar magabtana su kama ni ba, Ka kiyaye ni.
Sa'an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba! Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.