Maganarka da na samu na ci. Maganarka kuwa ta zama abar murna a gare ni, Ta faranta mini zuciya. Gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.
Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.
A fili yake, ku wasiƙa ce ta Almasihu, ta hannunmu, ba kuwa rubutun tawada ba ne, amma na Ruhun Allah Rayayye ne, ba kuwa a kan allunan dutse aka rubuta ta ba, sai dai a zuci.