Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zabura 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni, Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zabura 4:8
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare.


Na kwanta na yi barci, Na kuwa tashi lafiya lau, Gama Ubangiji yana kiyaye ni.


wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi.


Amma sa'ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, sa'ad da kuma ya ba ku hutawa daga maƙiyanku waɗanda suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya,


Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.


“A waccan rana zan yi alkawari Da namomin jeji, da tsuntsaye, Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra'ila. Zan kuma kakkarya baka da takobi, In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar, Sa'an nan za su yi zamansu lami lafiya.


Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”


“Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi.


Za ka nuna mini hanyar rai, Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki, Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.


Jama'ar da suka yi tafiya cikin duhu, Sun ga babban haske! Suka zauna a inuwar mutuwa, Amma yanzu haske ya haskaka su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ