Sa'ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa'ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.
Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.
Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!