Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na'am da shi, to, me zai sa sa'ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.
Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’
Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma'anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama'ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit.