6 An tanƙware ni, an ragargaza ni, Ina ta kuka dukan yini.
6 An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka.
Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba, Na tsaya a gaban taron jama'a, ina roƙon taimako.
Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan'uwa addu'a. Ina tafe a takure saboda makoki, Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.
Ga Allah wanda yake tsarona na ce, “Me ya sa ka manta da ni? Me ya sa nake ta shan wahala Saboda muguntar maƙiyana?”
Ya Allah, kai ne kake kāre ni, Me ya sa ka yashe ni? Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?
Me ya sa nake baƙin ciki haka? Me ya sa nake damuwa ƙwarai? Zan dogara ga Allah, Zan sāke yin yabonsa, Mai Cetona, Allahna.
Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala, Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.
Idanuna sun raunana saboda wahala. Ya Ubangiji, kowace rana ina kira gare ka, Ina ta da hannuwana zuwa gare ka da addu'a!
Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni, Damuwa ta fi ƙarfina. Sun yi wushefe a kan hanyata, Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.
Baƙin ciki ya gajerta kwanakina, Kuka kuma ya rage shekaruna. Na raunana saboda yawan wahalata, Har ƙasusuwana suna zozayewa!
Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki, Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana. Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.
Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi, Na kuwa yi kuka kamar kurciya, Idanuna sun gaji saboda duban sama. Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.
Jikina cike yake da tsutsotsi, Ƙuraje duka sun rufe shi, Daga miyakuna mugunya tana ta zuba.
Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu, Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.