Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.
Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe su Su zauna a tsattsarkan wurinka! Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka, Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!