Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba, Da bauta mai tsanani. Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma, Amma ba ta sami hutawa ba, Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.
Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.
Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.