8 Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, Bari yă sa wa jama'arsa albarka!
8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela
“Ni kaɗai ne Ubangiji, Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.
Amma ni zan raira yabbai gare ka, Zan miƙa maka sadaka, Zan cika wa'adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
Ubangiji ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku Tun daga ƙasar Masar. Banda ni ba ku san wani Allah ba, Banda ni kuma ba wani mai ceto.
suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”
Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,
Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”
Kana iya shirya dawakai don zuwa yaƙi, amma nasara ta Ubangiji ce.
Da Allah ya taso da Baransa, gare ku ne ya fara aiko shi, don yă yi muku albarka ta juyo da ko wannenku ga barin muguntarsa.”
Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada, Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa. Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin, Dukan jama'a su roƙi Allah yă sa musu albarka, Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.
Daga kan tuddai ba mu da wani taimako, Ko daga hayaniyar da ake yi a kan duwatsu, Daga wurin Ubangiji Allahnmu ne kaɗai taimakon Isra'ila yake fitowa.
Bayan wannan na ji kamar wata sowa mai ƙarfi ta ƙasaitaccen taro a Sama, suna cewa, “Halleluya! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu,
Ubangiji yana ba jama'arsa ƙarfi, Ya sa musu albarka da salama.
Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.
ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma riɓanya zuriyarka.”
Duk kuma lokacin da akwatin zai tashi, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji, ka sa maƙiyanka su warwatse, ka sa waɗanda suke ƙinka su gudu gabanka.”
Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta. Ya kuma kashe Filistiyawa. Ubangiji ya ba da babbar nasara.
Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji, Ka sa su sani su mutane ne kawai.
Ni, bawanka ne, Ka dube ni da alherinka, Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye, Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya.
Ni naka ne, ka cece ni! Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.