Zabura 27:6 - Littafi Mai Tsarki6 Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni. Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa! Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”