Kwana guda da za a yi a Haikalinka, Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam. Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna, Da in zauna a gidajen mugaye.
Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.
Saboda kuma ƙaunar Haikalin Allahna da nake yi, shi ya sa na ba da zinariyata da azurfata domin Haikalin Allahna, banda wanda na riga na tanada saboda Haikali mai tsarki.
Sa'an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa.
Sa'ad da Sulemanu ya gama yin addu'arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.