5 Ina ƙin tarayya da masu mugunta, Nakan kauce wa mugaye.
5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada, Amma ni na dogara gare ka.
Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.