Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.
A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne! Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta, Ba za a iya kaushe ta ba, Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”