Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta, Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama, Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar 'yan ƙananan ƙwari. Ya miƙa sararin sama kamar labule, Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.
Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.