Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.
Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.
Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce, “Ku yi godiya ga Ubangiji, Saboda madawwamiyar ƙaunarsa Tabbatacciya ce har abada.”
Sa'ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, 'yan kwanto, 'yan kwanton kuwa suka fatattake su.