5 Ina tafiya a kan tafarkinka kullum, Ban kuwa kauce ba.
5 Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.
Ba mu ci amanarka ba, Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.
Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta, Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.
Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari, Zai sa ka zauna lafiya.
Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata. Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!
Ka tsare ni, ba a kama ni ba, Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.
Na ce, “Ina kan fāɗuwa,” Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.
“Ya Ubangiji, na sani al'amuran mutum ba a hannunsa suke ba, Ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba
Da aminci ina bin hanyar da ya zaɓa, Ban kuwa taɓa kaucewa daga wannan gefe zuwa wancan ba.
Na kori magabtana, har na kama su, Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.