Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zabura 17:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ka san zuciyata, Kakan zo gare ni da dare, Ka riga ka jarraba ni sarai, Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba. Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zabura 17:3
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, Ka gwada muradina da tunanina.


Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,


Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi, Don kada harshena yă sa ni zunubi, Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”


Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.


Amma wa zai iya jurewa da ranar zuwansa? Wa kuma zai tsira sa'ad da ya bayyana? Zai zama kamar wutar da suke bauta ƙarfe, kamar kuma sabulu salo.


Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.


Ka jarraba mu, ya Allah, Kamar yadda ake tace azurfa da wuta, Haka nan ka jarraba mu.


Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.


Taku ta ƙare, ku masu shirya mugunta, Masu tsara mugunta a gadajensu! Sa'ad da gari ya waye, sai su aikata ta, Domin ikon aikatawa yana hannunsu.


Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu. Fushinsu na ci dare farai, Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.


Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.


Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.


Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni, Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.


Yana auna masu kirki da mugaye dukka, Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.


Idan na ci amanar abokina, Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,


Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci, Da dare kuma ya yi fashi.


Ubangiji dai zai sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma na ƙi in kashe wanda Ubangiji ya keɓe.


Ubangiji dai zai shara'anta tsakanina da kai, ya sāke mini, amma hannuna ba zai taɓa ka ba.


Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”


To, yau da idanunka ka ga yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a kogon, har waɗansu suka ce mini in kashe ka, amma na ji tausayinka. Na ce, ‘Ba zan miƙa hannuna in kashe ubangijina ba, gama shi keɓaɓɓe na Ubangiji ne.’


Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.


Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.


Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.


Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.


Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina, Gwada ni, ka gane damuwata.


Amma kai, ya Ubangiji, kana sane da ni, kana ganina, Kai kanka kake gwada tunanina. Ka jawo su kamar tumaki zuwa mayanka, Ka ware su domin ranar yanka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ