1 Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.
1 Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka.
Ka yi mini jinƙai, ya Allah, Gama mutane sun tasar mini, Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe!
Ka kiyaye ni kamar yadda ake kiyaye idanu, Ka ɓoye ni a inuwar fikafikanka,
Ubangiji yakan kiyaye kāsassu, Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.
Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka, Ya Allah Mai Runduna!
Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama'arsa duka! Ubangiji yana kiyaye masu aminci, Amma yakan hukunta masu girmankai da tsanani.
Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.
Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.
Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa,
Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.
Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka, Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata,
Waɗanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.
Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta. Yakan kiyaye rayukan jama'arsa, Yakan cece su daga ikon mugaye.
Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu, Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!
Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai, Ba ya rabuwa da amintattun jama'arsa, Yana kiyaye su koyaushe, Amma za a kori zuriyar mugaye.
Ka yi mini kāriya, ka cece ni, Gama na zo wurinka neman kāriya.
Ina tafiya a kan tafarkinka kullum, Ban kuwa kauce ba.
Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu.
Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji, Me ya sa bai cece ka ba? Idan Ubangiji na sonka, Don me bai taimake ka ba?”
Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni, Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni, A can za su yayyage ni kamar zaki.