Ku yi sowa ta farin ciki ya ku sammai! Ku yi sowa ku zurfafan wurare na duniya! Ku yi sowa ta murna, ku duwatsu, da kowane itace na jeji! Ubangiji ya fanshi mutanensa, Isra'ila, Saboda haka ya nuna girmansa.
Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya! Bari duwatsu su ɓarke da waƙa! Ubangiji zai ta'azantar da mutanensa, Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.
Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah, Bari mutanen Kedar su yabe shi! Bari su da suke zaune a birnin Sela Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!