5 Bari su duka su yabi sunan Ubangiji! Ya umarta, sai suka kasance.
5 Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.
“Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu, Kă sami ɗaukaka, da girma, da iko, Domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa, Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”
Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.”
Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama, Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya. Ya sa ruwan teku ya zo, Ya kwarara shi a bisa duniya. Sunansa Ubangiji ne!
Yana mulki bisa tekun da ya yi, Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.
Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku, Ku da kuke biyayya da umarnansa, Kuna kasa kunne ga maganarsa!