Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani.
Sa'an nan 'yan mata za su yi rawa da farin ciki, Samari da tsofaffi za su yi murna. Zan mai da makokinsu ya zama murna, Zan ta'azantar da su, in ba su farin ciki maimakon baƙin ciki.