1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ka yabi Ubanigji, ya raina!
1 Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina.
Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa, A duk inda yake mulki! Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi sunansa mai tsarki!
Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa, Su kuma kiyaye umarninsa. Ku yabi Ubangiji!
Da ma a hallakar da masu zunubi daga duniya, Da ma mugaye su ƙare ƙaƙaf! Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi Ubangiji!