9 Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji, Ka cece ni daga maƙiyana.
9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka.
Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.
Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako, Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni, Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.
Ka cece ni daga maƙiyana, ya Allahna, Ka kiyaye ni daga waɗanda suka tasar mini!
A ranar da na yi kira gare ka, Za a komar da abokan gābana baya, Gama na sani Allah yana tare da ni!
Kana lura da ni kullum, Ka cece ni daga magabtana, Daga waɗanda suke tsananta mini.
domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sākewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu ƙarfafa ƙwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai.
Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki, Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
Ka cece ni daga cikin wahalata, Sa'an nan zan yabe ka cikin taron jama'arka, Domin ka yi mini alheri.