9 Ka kiyaye ni daga tarkunan da suka kafa mini, Daga ashiftar masu aikata mugunta.
9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa.
Masu girmankai sun kafa mini tarko, Sun shimfiɗa ragar igiya, Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi.
Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.
Mugaye sun kafa mini tarko, Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.
Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna, Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni, Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
Bari a ji kururuwa daga gidajensu, Saboda maharan da ka aika musu farat ɗaya, Gama sun haƙa rami don in fāɗa, Sun kafa wa ƙafafuna tarkuna.
Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya, Ya san abin da zan yi. A kan hanyar da zan bi Maƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.
A shirye nake, ya Allah, Na shirya sosai! Zan raira waƙoƙi in yabe ka!
Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni, Ba wanda zai kiyaye ni, Ba kuwa wanda ya kula da ni.