3 Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina, Ka sa mai tsaro a leɓunana.
3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.
Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi, Don kada harshena yă sa ni zunubi, Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”
Kada ka dogara ga maƙwabcinka, Kada kuma ka amince da abokinka. Ka kuma kame bakinka daga matarka Wadda take kwance tare da kai.
Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.
To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.
Ina yabonka dukan yini, Ina shelar darajarka.
Na yi shiru, ban ce kome ba, Ko a kan abin da suke da kyau! Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi,