Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.
Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba'al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra'ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu,
Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.
Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.