“Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi, Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu. Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon, Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.
“Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau.