10 Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa, Ya karkashe sarakuna masu iko, wato
10 Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna,
Isra'ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa.
Haka fa suka kashe shi, shi da 'ya'yansa maza, da dukan jama'arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.