Mutanen Kiriyat-yeyarim kuwa suka zo suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji suka kai shi gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa, Ele'azara, ya lura da akwatin alkawarin Ubangiji.
Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.
Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Suka sa akwatin alkawari a sabuwar karusa. Uzza da Ahiyo, 'ya'yan Abinadeb, maza, suka bi da karusar da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo ne yake tafiya a gaban akwatin alkawarin.