3 Idan kana yin lissafin zunubanmu, Wa zai kuɓuta daga hukunci?
3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a, Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.
Amma mutane suna jin tsoronka! Wa zai iya tsayawa a gabanka Sa'ad da ka yi fushi?
don babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya jure mata?”
Jira kake ka ga ko zan yi zunubi, Don ka ƙi gafarta mini.
Amma wa zai iya jurewa da ranar zuwansa? Wa kuma zai tsira sa'ad da ya bayyana? Zai zama kamar wutar da suke bauta ƙarfe, kamar kuma sabulu salo.
Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.
Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu.
Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai? Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?
Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni, A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne. Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi.
Ka tuna da bayinka, su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kada ka kula da taurinkan jama'ar nan, ko muguntarsu, ko zunubansu
Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai mai adalci ne, gama ka bar mana ringin da ya tsira kamar yadda yake a yau. Ga mu nan gabanka da zunubinmu, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.”