6 Zan raira waƙa ga Ubangiji, Gama ya kyautata mini.
6 Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri.
Kada ki yi shakka, ya zuciyata, Gama Ubangiji yana yi mini alheri.
Ya Ubangiji, ka zo da ƙarfinka! Za mu raira waƙa mu yabi ikonka.
Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya, A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.
Arna sun haƙa rami sun kuwa fāɗa ciki, Sun ɗana tarko, ya kuwa kama su.
Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni. Na dogara gare shi. Ya taimake ni, don haka ina murna, Ina raira masa waƙoƙin yabo.