6 Ya kuma sa ka ka ga jikokinka! Salama ta kasance ga Isra'ila!
6 bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.
Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba'in bayan wannan, ya ga 'ya'yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu.
Yusufu fa ya ga 'ya'yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi 'ya'yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu.
Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu, Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta! Salama ta kasance tare da Isra'ila!
bayyana Ɗansa a gare ni, domin in sanar da shi ga al'ummai, ban yi shawara da ɗan adam ba,
Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al'ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.
Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.
Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na 'ya'yanka.”