Muka kuwa tashi daga kogin Ahawa a ran goma sha biyu ga watan ɗaya, don mu tafi Urushalima, Allahnmu kuma yana tare da mu, ya kuwa cece mu daga hannun maƙiyanmu, da mafasa a hanya.
A dā sa'ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra'ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama'ata Isra'ila, za ka zama sarkinsu.’ ”