Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”
Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.