Matalauta da 'yan ƙaƙa naka yi sun sheƙa zuwa wurinka, Sun sami zaman lafiya a lokatan wahala. Ka ba su mafaka daga hadura, Ka inuwantar da su daga matsanancin zafi. Mugaye sukan tasar musu kamar hadirin ƙanƙara,
Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.
“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!