3 Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba.
Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe.
“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.
ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.
Za su ɗauke ka a hannuwansu, Don kada ka buga ƙafarka a dutse.
Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba, Aikin magina banza ne. Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba, Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.
wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.
Shi ne yake rayar da mu, Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.
Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.
Ubangiji zai kiyaye shi, yă keɓe ransa. Ubangiji zai sa yă ji daɗi a ƙasar, Ba zai bar shi a hannun magabtansa ba.
Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.