2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.
Ni ne Ubangiji Allahnku, Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”
Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi wanda ya yi sama da duniya.
Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji shi ne mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.
Amma Ubangiji kana tare da ni Kamar jarumi mai bantsoro, Don haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe, Ba za su rinjaye ni ba. Za su sha kunya ƙwarai, Gama ba za su yi nasara ba. Ba za a manta da su ba.
Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasa Ya sa muku albarka!
“Zan hallaka ku, ya mutanen Isra'ila! Wane ne zai taimake ku?
A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,