1 Na duba wajen duwatsu, Daga ina taimakona zai zo?
1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?
Sa'ad da nake shan wahala, Na yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa amsa mini.
Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka, A Sama inda kake mulki.
Daga kan tuddai ba mu da wani taimako, Ko daga hayaniyar da ake yi a kan duwatsu, Daga wurin Ubangiji Allahnmu ne kaɗai taimakon Isra'ila yake fitowa.
Jama'arsu za su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”
Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka, Na naɗa sarkina.”
Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,
A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza. Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.