Zabura 12:4 - Littafi Mai Tsarki4 Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama, Ba kuwa wanda zai hana mu. Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”