4 Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce, “Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
4 Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
“Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji! Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu! Ku yi masa sujada, ku jama'ar Isra'ila!
Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa, Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
Ubangiji nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce, Amincinsa kuwa har abada abadin ne.
Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama'ar Isra'ila! Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne, Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.