Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama'arka masifa.
Sai firistoci masu hidimar Ubangiji, Su yi kuka a tsakanin shirayi da bagade, Su ce, “Ya Ubangiji, ka ceci jama'arka, Kada ka bar gādonka ya zama abin zargi Da abin ba'a a tsakiyar al'ummai. Don kada al'ummai su ce, ‘Ina Allahnsu?’ ”
Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.