8 Yakan sa su zama abokan sarakuna, Sarakunan jama'arsa.
8 ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.
Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya, Yakan kafa su har abada tare da sarakuna, A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.
Za ka haifi 'ya'ya maza da yawa, Waɗanda za su maye matsayin kakanninka, Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.
Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.”
Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa, Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya. (Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)
Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.