Dukan itatuwan jeji za su sani, Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana, In sa ƙanana kuma su zama manya, In sa ɗanyen itace ya bushe, In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”
Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.
“Tun da yake na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaban jama'ata Isra'ila, kai kuwa ka bi hanyar Yerobowam, ka sa jama'ata, wato Isra'ila, su yi zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu,