“Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.
Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya! Bari duwatsu su ɓarke da waƙa! Ubangiji zai ta'azantar da mutanensa, Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.
Saboda haka waɗanda suke yamma za su ji tsoron sunan Ubangiji, waɗanda suke wajen gabas kuma za su ji tsoron ɗaukakarsa, gama zai zo kamar rafi mai tsananin gudu, wanda iskar Ubangiji take korawa.
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
Daga manisantan wurare na duniya za mu ji waƙoƙin yabon Isra'ila, al'umma adala. Amma ba ni da sauran sa zuciya! Lalacewa nake yi! Maciya amana suna ta cin amana, cin amanarsu sai gaba gaba yake yi.