1 Yabo Ya tabbata ga Ubangiji! Ku bayin Ubangiji, Ku yabi sunansa!
1 Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.
Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka, Jama'arka kuma za su yi maka godiya!
Ku yabi Ubangiji, ya ku Lawiyawa, Ku yabe shi, dukanku da kuke tsoronsa!
Ku zo mu yabi Ubangiji, Dukanku bayinsa, Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima, A cikin Haikalinsa da dare.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa.
Zuriyar bayinsa za su gāje ta, Masu ƙaunarsa za su zauna a wurin.
Ubangiji zai fanshi bayinsa, Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafaka Za a bar su da rai.
Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa, Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”