3 Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya, Adalcinsa zai tabbata har abada.
3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada.
Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa'ad da wahala ta zo.
Hikima takan tsawanta ranka, ta kuma ba ka dukiya da daraja.
Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.
zai kuma sa aminci cikin al'ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama'arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.
Yakan bayar ga matalauta hannu sake, Alherinsa kuwa dawwamamme ne. Zai zama mai iko wanda ake girmamawa.
kamar muna baƙin ciki, kullum kuwa farin ciki muke yi, kamar matalauta muke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji, Yakan ba da kyakkyawar ganewa Ga dukan waɗanda suke bin umarnansa, Sai ku yabe shi har abada!
Dukan abin da yake yi, Cike yake da girma da ɗaukaka, Adalcinsa har abada ne.
Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye! Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata za ta kasance har abada abadin.”
Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.
Sa'an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka, A sa'ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya.
Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa, Amma masu biyayya ga Ubangiji, Ba abu mai kyau da sukan rasa.
Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni, Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.
Mutane masu hikima suna zaune da wadata da nishaɗi, amma wawaye da zarar sun sami kuɗi sukan kashe su nan da nan.