Waɗanda suke ƙina ba dalili Sun fi gashin kaina yawa, Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina, Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni. Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.
Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi, Jama'ar Isra'ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta, Yahuza kuma ta tayar wa Allah, Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.
Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.