2 Ku farka, ya molona da garayata! Zan farkar da rana!
2 Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.
Zan raira waƙar yabo ga Allah, Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,
A fara waƙa, ku buga bandiri, Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.
Ka farka, ya raina! Ku farka, molona da garayata! Zan sa rana ta farka!
Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya. Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.
Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa, A duk inda yake mulki! Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba! Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba! Ka ci gaba, kai Barak, Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba!